’Yan majalisar dokokin Jihar Zamfara takwas da suka fice daga jam’iyyar APC a makonnin baya sun yanke shawarar komawa jam’iyyar bayan ganawa da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Rahotanni sun ce ’yan majalisar sun gana da Tinubu ne a daren Lahadi, inda suka amince su koma APC domin taimaka wa jam’iyyar a zaɓen shekarar 2027.
Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ne ya jagoranci tawagar zuwa wurin shugaban ƙasar, tare da ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya, Aminu Sani Jaji.
- Jami’an tsaro sun kama mutane 430, ciki har da mata 50, a Yamai
- Tinubu ya karɓi tawagar APC daga Zamfara a Fadar Shugaban Ƙasa
Wannan mataki ya zo ne duk da rahotannin da suka nuna cewa ’yan majalisar na shirin komawa jam’iyyar ADC mai adawa.
Rahoton ya ce ana ƙoƙarin shawo kan korafe-korafensu bayan ganawar da suka yi da Tinubu.
’Yan majalisar takwas sun haɗa da Aliyu Ango Kagara mai wakiltar Talata Mafara ta Kudu, Ibrahim Tukur Bakura na Bakura, Faruk Musa Dosara na Maradun I, Bashir Abubakar Masama na Bukkuyum ta Arewa, Muktaru Nasiru Kaura na Kaura ta Arewa, Nasiru Abdullahi na Maru ta Arewa, Bashar Bello na Bungudu ta Yamma da Bashar Aliyu na Gummi I.
Sai dai har yanzu bayanin da aka bayar bai fayyace korafe-korafen ’yan majalisar ko matakan da aka ɗauka domin warware su ba.