Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya zargi jam’iyyar APC da kasa samar da cikakken bayani kan harin da ka kai wa masu zanga-zangar #EndSARS a Lekki da ke Legas, shekaru shida bayan faruwar lamarin.
Atiku ya ce har yanzu ’yan Najeriya na jiran amsar tambayar wanda ya bayar da umarnin kai harin kan masu zanga-zangar a watan Oktoban 2020.
Ya kuma tuna da kalaman shuganan kasa Bola Tinubu a lokacin, inda ya tambayi irin mutanen da suka halarci wurin da kuma tsawon lokacin da suka yi a wurin.
- Amnesty International ta bukaci a dauki mataki kan zargin kashe fararen hula da ’yan sanda ke yi
- DSS ta gurfanar da mutum biyar kan sace ɗaliban NYSC 20 a Imo
- Tinubu ya ce ba zai dawo da tallafin man fetur ba
Ya ce rashin samun amsoshin ya ƙara jefa iyalan waɗanda abin ya shafa da matasa cikin rashin yarda da hukumomi, yana mai cewa gwamnati na da alhakin kare rayukan ’yan ƙasa da tabbatar da ɗaukar alhaki.
Atiku ya kuma danganta matsin tattalin arzikin da matasa ke fuskanta da tsadar man fetur da raguwar damar samun abin dogaro da kai.
Ya ba da misalin wata mata da ya ce ta yi murabus daga aikinta a wannan watan saboda albashinta bai isa kuɗin zirga-zirgar zuwa wurin aikinta ba.
Ya ce shirin farfaɗo da tattalin arzikinsa na da nufin rage tsadar rayuwa ta hanyar tallafin man fetur da aka tace a Najeriya, da ƙara samar da kayayyaki a cikin gida, da tallafa wa masu ƙaramin albashi da ɗalibai, da rage almubazzaranci maimakon ƙara haraji.
Atiku ya jaddada cewa matasan Najeriya sun cancanci sanin gaskiyar abin da ya faru a Lekki da samun tattalin arzikin da zai ba su damar inganta rayuwarsu, yana mai cewa bayan shekaru shida na mulkin APC, ’yan Najeriya na da haƙƙin tambayar dalilin da ya sa har yanzu ba a samu amsoshi da damammaki da suke nema ba.