Rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta ce ta kama mutane 11 da ake zargi da hannu a fashi da makami da kuma damfarar fasinjoji ta hanyar amfani da motoci, tare da ƙwato wayoyin hannu 38 da kwamfutoci uku.
Kwamishinan ’yan sandan FCT, Ahmed Muhammed Sanusi, ya bayyana cewa an kama wasu mutane biyu a ranar 17 ga Satumba, 2026, a kan hanyar AYA zuwa Nyanya, ya ce ana zargin ƙungiyar tasu tana kai hare-hare a Abuja da wasu sassan jihohin Nasarawa, Neja da Kogi.
An ƙwato bindigogi ƙirar gida uku, harsasai uku, wuƙaƙe huɗu, wayoyin hannu 17, adduna biyu da na’urar karɓar kuɗi ta POS a hannunsu.
- ADC ta ce kalaman Yari sun nuna gazawar APC wajen magance matsalar tsaro
- ’Yan sanda sun kama waɗanda ake zargi da fashi, kisan kai da safarar miyagun ƙwayoyi a Bauchi
A wani lamari kuma, rundunar ta kama wani mutum bayan an kai ƙara kan fashi da makami da aka ce ya faru a ranar 26 ga Satumba a yankin Jabi.
Ana zargin wanda aka kama da rufe fuskarsa da abin rufe fuska, da yi wa wata mata duka da barazanar da wuƙa, tare da kwace mata jakar hannu mai ɗauke da iPhone da wasu kayayyaki.

Sanarwar ta ce ya kuma cire kuɗi daga asusun bankunanta ta amfani da wayarta da katin ATM. Daga gidansa an ƙwato wasu kayayyaki da suka haɗa da wuƙa, abin rufe fuska da katin zaɓe.
Kwamishinan ya ce a wani bincike kan ƙungiyar “one chance”, wato masu amfani da motoci wajen damfarar fasinjoji, an kama mutane takwas bayan wata mata, matar wani ɗan sanda, ta hau motar haya a mahadar AYA a ranar 7 ga Agusta, 2026.
Ana zargin waɗanda suka ɗauke ta sun kwace mata waya da sauran kayayyaki, sannan suka tura kuɗinta zuwa asusunsu. Binciken ta hanyar na’urorin zamani ya taimaka wajen gano waɗanda ake zargi da kuma bin diddigin mu’amalolin kuɗin.
Rundunar ta ce an ƙwato wayoyin hannu 21 da kwamfutoci uku a binciken, ciki har da na matar da lamarin ya shafa.
Ta kuma ce bincike ya nuna cewa ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin yana sauya lambobin IMEI na wayoyin sata domin sayar da su ba tare da an gano asalinsu ba.
Kwamishinan ya ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin a kotu bayan kammala bincike, tare da kira ga mazauna Abuja su riƙa kai rahoton abubuwan da suka shige musu duhu ga jami’an tsaro.