Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da samun mutum ɗaya da ya kamu da cutar Ebola a Babban Birnin Tarayya, Abuja, bayan gwaje-gwajen dakin bincike sun tabbatar da cutar a ranar 20 ga Oktoba, 2026.
A cikin sanarwar da Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya fitar, ya ce majinyaciyar mata ce da ta shigo Najeriya daga Uganda ta jirgin sama na ƙasa da ƙasa an kwantar da ita a wani asibiti mai zaman kansa a Abuja, kuma a halin yanzu tana killace tare da samun kulawar likitoci.
Gwamnatin ta ce an fara gano mutane 44 da suka yi mu’amala ta kusa da majinyaciyar domin bibiyar waɗanda ka iya kamuwa da cutar.
- ’Yan sanda sun kama waɗanda ake zargi da fashi, kisan kai da safarar miyagun ƙwayoyi a Bauchi
- ’Yan sanda sun kama mutane 11 da ake zargi da fashi da makami da damfarar fasinjoji a Abuja
Ana kuma ƙara sa ido kan ma’aikatan lafiya, majinyata, masu kula da ita da sauran mutanen da ka iya fuskantar haɗarin kamuwa da cutar.
Sanarwar ta ce Ebola na yaɗuwa ne ta hanyar taɓa jini ko ruwan jikin mutumin da ya kamu da cutar ko wanda ya mutu sanadiyyarta, da kuma kayan da suka gurɓace.
Ba ta yaɗuwa daga mutum kafin bayyanar alamominta, waɗanda suka haɗa da zazzaɓi, matsananciyar kasala, ciwon kai, amai da gudawa.
Gwamnatin ta buƙaci jama’a su riƙa wanke hannu akai-akai, su guji taɓa ruwan jikin wanda ake zargin ya kamu da cutar, kuma su kai rahoton duk wani alamu ga hukumomin lafiya.
Ta kuma shawarci duk wanda ya fara nuna alamomin cutar da ya guji kusanci da wasu tare da kiran jami’an lafiya domin samun jagoranci kafin zuwa asibiti.
Gwamnatin ta ce tana aiki tare da hukumomin lafiya domin dakile yaɗuwar cutar, tana mai kira ga jama’a da su guji yaɗa jita-jita.