Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC Limited) ya ɗage taron shugabannin kamfanonin da ke kwangila da shi da abokan hulɗarsa kan lafiya, tsaro da muhalli (HSE), wanda aka shirya gudanarwa a Abuja daga ranar 21 zuwa 22 ga Oktoba, 2026.
Kamfanin ya ce an ɗauki matakin ne a matsayin rigakafi bayan tabbatar da bullar cutar Ebola a Abuja.
- APC ta fara shirye-shiryen yaƙin neman zaɓen Shugaba Tinubu
- Shettima ya kafa kwamitin bunkasa kiwo da noman kayan abinci a Najeriya
NNPC ya bayyana cewa lafiyar mahalarta taron da tsaronsu da walwalarsu su ne babban abin da yake ba fifiko.
Kamfanin ya nemi afuwar duk wani tsaiko da ɗage taron zai haifar, tare da gode wa abokan hulɗarsa, ’yan kwangila, masu gabatar da jawabai da sauran mahalarta bisa fahimta da haƙurinsu.
NNPC ya ce zai sanar da sabuwar ranar gudanar da taron nan gaba.