Majalisar Wakilan Najeriya ta ɗauki matakan sake duba wasu ƙudurin dokoki tare da bayar da umarnin binciken ayyukan kasuwanci da gine-ginen da ba a ba da izini ba a kusa da gadojin gwamnatin tarayya a Jihar Legas.
A zaman majalisar na ranar Talata, 20 ga Oktoba, 2026, ta umarci kwamitocin da suka dace su binciki takardar umarnin Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF) da ke buƙatar jami’ai da ’yan Majalisar Tarayya su nemi izini kafin yin tafiye-tafiyen aiki zuwa ƙasashen waje.
- Shettima ya kafa kwamitin bunkasa kiwo da noman kayan abinci a Najeriya
- APC ta fara shirye-shiryen yaƙin neman zaɓen Shugaba Tinubu
Majalisar ta kuma mayar da kudirin gyaran dokar kafa Hukumar Fansho ta Ma’aikatan Majalisar Tarayya ta shekarar 2026 ga kwamitin cikakkiyar majalisa, bayan nazarin fasaha ya gano matsalolin shari’a, gudanarwa da kundin tsarin mulki a sashe na 7 da na 8.
Haka kuma, majalisar ta ɗauki matakin sake duba kudirin dokar kafa Hukumar Kula da Keɓe Kayayyakin Noma ta Najeriya ta shekarar 2026, tare da miƙa shi ga kwamitin majalisa domin ƙarin nazari.
Dangane da gadoji, majalisar ta umarci kwamitocin ayyukan gine-gine da kadarorin gwamnati su binciki gine-gine da harkokin kasuwanci da ba a ba da izini ba a kusa da gadar Eko da sauran gadojin gwamnatin tarayya a Legas, domin tantance bin dokoki da kuma ba da shawarwarin kare kayayyakin more rayuwar jama’a.