Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya buƙaci kafafen yaɗa labarai su rungumi basirar AI da sabbin fasahohin zamani, tare da kiyaye ƙa’idojin aikin jarida da ’yancin editoci.
Ministan ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Alhamis, yayin ƙaddamar da sabon tsarin haɗa sassan aikin jarida na jarida, rediyo, talabijin da kafafen intanet na kamfanin Media Trust Group.
Ya ce haɗa waɗannan sassa zai taimaka wa kafafen yaɗa labarai wajen biyan buƙatun masu sauraro da masu karatu da ke sauyawa, sai dai ya jaddada cewa amfani da fasaha bai kamata ya rage muhimmancin hukuncin ƙwararrun ’yan jarida, ɗabi’ar aiki da alhakin bil’adama ba.
- Babban Bankin Najeriya ya tattauna da ’yan kasuwa kan sauƙaƙa biyan kuɗi tsakanin Najeriya da China
- Majalisar Wakilai ta nemi a koma kan asalin hanyar Lagos–Calabar
Yayin da zaɓen 2027 ke gabatowa, Idris ya buƙaci kafafen yaɗa labarai su ba da fifiko ga sahihanci, adalci da tantance bayanai, tare da guje wa yaɗa labaran ƙarya.
Ya yi gargaɗin cewa hotuna da bidiyoyin bogi da AI ke samarwa na iya raunana amincewar jama’a da bayanai.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, da Gwamnan Jigawa, Umar Namadi, sun yaba wa Media Trust Group kan rungumar fasaha da gudummawar da take bayarwa wajen samar da ayyukan yi.
Darakta-Janar na NITDA, Kashifu Inuwa Abdullahi, ya kuma bukaci ’yan jarida su yi amfani da AI wajen tantance sahihancin bayanai maimakon dogaro da ita a matsayin madadin ƙwarewar ɗan Adam.
Ministan ya bukaci kamfanin ya ci gaba da amfani da sabon tsarin wajen ƙarfafa binciken jarida da samar da sahihan labarai cikin ɗaukar nauyi, yana mai cewa aikin jarida na iya taimaka wa al’umma ba tare da rasa ’yancin yin bincike da sukar hukumomi ba.