Majalisar Wakilai ta Najeriya ta ɗauki matakan ƙarfafa bin dokokin sufuri ta ruwa da kuma kare hanyoyin haɗin kai tsakanin al’ummomin gabar teku, ciki har da neman a sake duba shirin sauya babbar hanyar Lagos–Calabar Coastal Highway.
A zaman majalisar na ranar Laraba, an mayar da ƙudirin binciken yadda kamfanonin sufuri ta ruwa ke bin dokokin cabotage, dokokin bai wa ’yan Najeriya dama da kuma biyan haraji zuwa wani kwamitin musamman domin gudanar da bincike.
Binciken zai duba yadda ake ɗaukar ma’aikatan ƙasashen waje, mamayar kasuwa, bayyana farashin ayyuka da kuma damar da ƙwararrun ’yan Najeriya ke samu a masana’antar sufuri ta ruwa.
- Akpabio ya buƙaci Birtaniya ta ƙara zuba jari a mai, gas da ma’adinan Najeriya
- Atiku ya nemi Tinubu ya yi bayanin inda Naira biliyan 10 na yaƙi da Ebola suka shiga
A wani ƙudiri kuma, majalisar ta buƙaci a kiyaye hanyar Coastal Highway da ta ratsa wasu al’ummomi a jihohin Ondo da Delta, ciki har da hanyar Escravos–Ogheye–Ugborodo.
Majalisar ta kuma nemi a gudanar da bincike mai zaman kansa kan wasu hanyoyin da ake tunanin bi, tare da tantance yiwuwar aikin ta fuskar injiniyanci, tasirinsa ga muhalli da tattalin arzikin al’umma, kuɗin da zai ci da kuma amfanin da za a samu.
Matakan na nufin ƙarfafa shigar ’yan Najeriya cikin masana’antar sufuri ta ruwa, samar da ayyukan yi ga ’yan ƙasa da kuma kare damar al’ummomin gabar teku na samun muhimman hanyoyin ci gaban tattalin arziki.