Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya nemi ƙarfafa haɗin gwiwar Najeriya da Birtaniya a harkokin majalisa, dimokuraɗiyya da zuba jari, musamman a fannonin mai, gas da ma’adinai.
Akpabio ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi Babban Kwamishinan Birtaniya a Najeriya, Peter Vowles, wanda ya kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa da ke Majalisar Ƙasa a Abuja.
Ya ce tattaunawar tasu ta mayar da hankali kan ƙarfafa alaƙar Majalisar Ƙasa ta Najeriya da Majalisar Dokokin Birtaniya, ta hanyar musayar ƙwarewa, haɗin gwiwar hukumomi da koyon ingantattun hanyoyin gudanar da ayyukan majalisa.
- ’Yan sanda sun kama makanikin da ake zargi da satar mota ta Naira miliyan 8 a Kano
- Sokoto ta lashe lambar yabo a fannin ilimin dijital a Najeriya
Shugaban majalisar ya jaddada muhimmancin ƙara hulɗa tsakanin ’yan majalisar Najeriya da takwarorinsu na Majalisar Wakilai da ta Iyayengijirsu Birtaniya, domin inganta dokoki da ƙarfafa cibiyoyin dimokuraɗiyya.
Akpabio ya kuma bukaci ’yan kasuwar Birtaniya su ƙara zuba jari a Najeriya, yana mai cewa sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa na samar da damammaki ga masu neman zuba jari na dogon lokaci.
Ya kuma yaba da alakar da ke tsakanin ƙasashen biyu, ciki har da tarbar da Sarki Charles III ya yi wa Tinubu a ziyarar aiki da ya kai Birtaniya.
Ya ce ya ji daɗin tabbacin da babban kwamishinan ya bayar na ƙarfafa dangantakar Birtaniya da Najeriya da kuma tallafa wa ayyukan Majalisar Ƙasa, yana mai cewa haɗin gwiwar ya kamata ya haifar da ƙarfafa dimokuraɗiyya da ci gaban ƙasa.