Kwamishinan ’yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya gargaɗi jami’an ’yan sanda masu shirin kammala horo da su kasance masu ladabi, biyayya da gaskiya wajen gudanar da aikinsu.

Ya yi wannan gargaɗi ne a ranar Alhamis, 22 ga Oktoba, 2026, yayin da yake gabatar da lacca ga ɗaliban jami’an ’yan sanda masu muƙamin ASP a rukuni na 8 a Kwalejin ’Yan Sandan Najeriya da ke Wudil.

Laccar, mai taken “Daga Alamar Muƙami zuwa Babban Matsayi: Shekaru 30 na Ladabi, Biyayya da Tsare-tsaren Aikin ’Yan Sanda a Najeriya”, ta mayar da hankali kan ƙwarewa, ɗabi’a da jagoranci.

Bakori ya bayyana cewa ya fara aikinsa a rundunar ’yan sanda a wannan kwaleji a ranar 15 ga Agusta, 1996, a matsayin ɗalibin ASP.

Kwamishinan ya ce aikin ’yan sanda a wannan zamani ya wuce amfani da ƙarfi kawai, domin yana buƙatar amfani da bayanan sirri, fasaha, mutunta haƙƙin ɗan Adam da bin ƙa’idojin dimokuraɗiyya.

Ya kuma shawarci ɗaliban da su kasance masu koyo a kowane lokaci tare da ƙara iliminsu domin inganta ƙwarewa da damar samun ci gaba a aiki.

Da yake magana kan tsaron Kano, Bakori ya ce rundunarsa na amfani da dabarun samar da tsaro ta hanyar haɗin gwiwa da al’umma, tattara bayanan sirri, nazarin wuraren da ake aikata laifuka da haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro.

Ya bayyana Operation Kukan Kura a matsayin wani samfurin aiki da ke amfani da bayanan sirri da goyon bayan al’umma wajen rage daba da sauran laifuka a jiahr Kano.

Bakori ya jaddada cewa ladabi, riƙon amana da gaskiya su ne ginshiƙan samun amincewar jama’a, ya buƙaci ɗaliban da su kiyaye mutuncinsu, su ba manyansu shawarwari na gaskiya da ƙwarewa, tare da tuna cewa samun matsayi ba ya nufin mutum ya samu girmamawa kai tsaye, domin ana samun ta ne ta hanyar aiki tuƙuru da kyawawan ɗabi’u.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *