Najeriya da Rwanda sun amince da ƙarfafa haɗin gwiwar sojojinsu, inganta ƙwarewar gudanar da ayyukan tsaro da kuma samar da hanyoyin magance matsalolin tsaron Afirka ƙarƙashin jagorancin ƙasashen nahiyar.

Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, da Hafsan Sojin Rwanda, Manjo Janar Vincent Nyakarundi, ne suka bayyana hakan yayin wani liyafar cin abinci da rundunar tsaron Rwanda ta shirya domin girmama tawagar Najeriya, a ƙarshen ziyarar aiki ta kwanaki biyar da Shaibu ya kai ƙasar.

Shaibu ya ce ta’addanci, tsattsauran ra’ayi mai nasaba da tashin hankali, aikata manyan laifuffuka a ƙasashe daban-daban da kuma yaɗuwar makamai ba bisa ƙa’ida ba na buƙatar ƙarfafa haɗin gwiwar sojoji, musayar bayanan sirri da kuma haɗin gwiwar ƙasashen Afirka wajen magance matsalolin.

Ya bayyana cewa ƙwarewar Najeriya wajen yaƙi da ta’addanci da tawaye, tare da ƙwarewar Rwanda a ayyukan wanzar da zaman lafiya da sake gina yankunan da rikici ya shafa, za su samar da ingantaccen tushe na haɗin gwiwa.

Ya lissafa horar da sojoji, musayar ƙwarewa, atisayen haɗin gwiwa, musayar bayanan sirri, tsaron intanet, jiragen saman soji da bunƙasa fasahar ƙera kayan aikin tsaro a matsayin muhimman fannoni.

Shaibu ya kuma jaddada muhimmancin amfani da sabbin fasahohi, musamman jiragen sama marasa matuƙa, ingantattun na’urorin sa ido da basirar AI, domin ƙara ingancin ayyukan soji da rage dogaro da ƙasashen waje.

A nasa ɓangaren, Nyakarundi ya yaba da ziyarar, yana mai cewa za ta ƙarfafa dangantakar soji tsakanin ƙasashen biyu tare da samar da haɗin gwiwa mai amfani.

Shugabannin sojojin biyu sun sake tabbatar da aniyarsu ta mayar da sakamakon ziyarar zuwa ayyukan zahiri da za su ƙara shirin ko-ta-kwana da ƙwarewar rundunoninsu, tare da inganta tsaron Afirka baki ɗaya.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *