Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inda suka tattauna batutuwan ƙasa da hanyoyin bunƙasa Jihar Gombe da Arewacin Najeriya.

Gwamnan ya bayyana cewa tattaunawar ta mayar da hankali kan fannoni da ke buƙatar tallafin gwamnatin tarayya da ƙarfafa haɗin gwiwa domin hanzarta ci gaba da inganta rayuwar al’umma.

Inuwa Yahaya, wanda kuma shi ne shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya, ya ce ya gabatar da batutuwan da suka shafi yankin Arewa baki ɗaya, tare da jaddada buƙatar ci gaba da tattaunawa da haɗa kai wajen magance ƙalubalen yankin.

Gwamnan ya gode wa Tinubu bisa karɓar sa da kuma sauraron batutuwan da ya gabatar yayin ganawar.

Ya kuma jaddada aniyarsa ta ƙarfafa hulɗa da gwamnatin tarayya da neman ayyukan tallafi da za su kawo ci gaba mai ma’ana ga Jihar Gombe, yankin Arewa maso Gabas da Arewacin Najeriya baki ɗaya.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *