Rundunar ’yan sandan jihar Yobe ta kama mutane uku da ake zargi da haɗa baki wajen satar kayan aikin gona da kuma karɓar kayayyakin da aka sace a yankin Garin Alkali, ƙaramar hukumar Bursari ta jihar.
A ranar 21 ga Oktoba, 2026, ofishin ’yan sandan Garin Alkali ya samu kiran gaggawa cewa wasu mutane sun cafke wani mutum mai shekara 40 a wani gona da ke kusa da ƙauyen Tarabutu bisa zargin satar kayan aikin gona.
Jami’an ’yan sanda sun isa wurin tare da ɗaukar wanda ake zargin domin gudanar da bincike.
- Sheikh Musa Ayuba Lukuwa ya zargi gwamnatin Sakkwato da sakin wanda ya yi barazanar kashe shi
- Gwamnatin Jihar Katsina ta ƙaddamar da tashar wutar lantarki mai ƙarfin 120MVA a Kankia
A yayin tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa cewa ya haɗa baki da wasu mutane biyu wajen satar kayan aikin gona a yankin gonakin Duhuwu Nima, ya kuma bayyana cewa an sayar da kayan da aka sace ga wani mutum a Gashua, lamarin da ya sa jami’an ’yan sanda suka bi sawunsa tare da kama shi.
Binciken da aka gudanar a gidan wanda ake zargin karɓar kayan da aka sace ya kai ga gano janareto biyu masu aikin famfo ruwa, bututun fitar da ruwa, silindar gas biyu da kuma na’urorin hasken rana guda 10, waɗanda ake zargin kayan sata ne.
A ranar 22 ga Oktoba, jami’an ’yan sandan sun kuma kama wani mutum da ake zargi da hannu a satar, wanda shi ma ya amsa zargin. Rundunar ta ce ana ci gaba da ƙoƙarin kama sauran wanda ake zargi, yayin da bincike ke gudana.
Kwamishinan ’yan sandan jihar Yobe, Usman Kanfani Jibrin, ya yi kira ga manoma da sauran al’umma da su riƙa kai rahoton duk wani abu da suka zargi ba da jimawa ba.