Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation WHIRL STROKE sun hana wasu da ake zargi da garkuwa da mutane sace matafiya biyu, tare da kuɓutar da su a kan hanyar Naka zuwa Ahume a Jihar Benue.

Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce lamarin ya faru ne ranar 24 ga Oktoba, 2026, lokacin da sojojin ke gudanar da sintiri suka ci karo da waɗanda ake zargin masu garkuwa ne, ɗauke da makamai, suna ƙoƙarin sace masu ababen hawa da sauran matafiya.

Sojojin sun yi musayar wuta da waɗanda ake zargin, lamarin da ya tilasta musu barin waɗanda suka yi garkuwa da su tare da tserewa.

Ɗaya daga cikin waɗanda aka ceto, Mngunengen Ihom, mai shekaru 36, ’yar Ahume, ta samu raunin sara da adda a yayin lamarin.

An garzaya da ita zuwa Babban Asibitin Naka domin samun kulawar likitoci.

Kwamandan rundunar haɗin gwiwar, Manjo Janar Moses Gara, ya umarci sojoji su ƙara ƙaimi wajen gudanar da ayyukan tsaro bisa sahihan bayanan sirri, tare da ƙarfafa tattara bayanan sirri domin gano barazana da wuri.

Ya kuma buƙaci jama’a su riƙa kai wa hukumomin tsaro bayanan da suka dace domin tallafa wa ayyukan dawo da zaman lafiya.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *