Shugaban rundunar sojojin ƙasa ta Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya halarci buɗe baje kolin kayayyakin tsaro na ƙasashen Afirka, AFRIDEX 2026, da aka gudanar a Legas ranar Litinin, 26 ga Oktoba.
Taron ya haɗa shugabannin Afirka, manyan jami’an soji, masana tsaro da kamfanonin kera kayan yaƙi domin tattauna sabbin hanyoyin tunkarar ƙalubalen tsaro da ke fuskantar nahiyar.
- JIBWIS ta kare kanta kan zargin alaƙa da kalaman tashin hankali
- NYSC za ta ƙarfafa matakan kare lafiyar ma’aikata da ’yan bautar ƙasa
Wakilan Shugaba Bola Ahmed Tinubu kuma Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, na cikin manyan baki da suka halarci taron, wanda ke da manufar ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da bunƙasa sabbin fasahohi.
An shirya AFRIDEX 2026 ne domin baje kolin sabbin fasahohin tsaro, ƙarfafa ƙera kayan tsaro a cikin Afirka, sauƙaƙa musayar fasaha da faɗaɗa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen nahiyar da abokan hulɗarsu na ƙasashen waje.
Baje kolin ya kuma mayar da hankali kan samar da hanyoyin haɗin gwiwa wajen tunkarar barazanar tsaro da ta ratsa iyakokin ƙasashe, yaƙe-yaƙen da ba na gargajiya ba da sauran sabbin ƙalubalen tsaro a Afirka.