Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya buƙaci Jamus ta ƙara zuba jari a masana’antu, samar da lantarki, noma da fasaha a Najeriya domin ƙirƙirar ayyukan yi da bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.

Akpabio ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi tawagar Kwamitin Haɗin Gwiwar Tattalin Arziki da Ci Gaba na Majalisar Dokokin Jamus, ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Farfesa Wolfgang Stefinger, a ofishinsa da ke Majalisar Ƙasa a Abuja.

Ya ce Najeriya da Jamus sun shafe sama da shekaru 60 suna hulɗa, amma ya kamata a mayar da wannan dangantaka zuwa ayyukan da za su samar da masana’antu, jawo jarin ƙasashen waje, samar da ayyukan yi da inganta rayuwar jama’a.

Shugaban majalisar ya kuma jaddada muhimmancin samar da ingantacciyar wutar lantarki ga masana’antu, yana mai buƙatar a gaggauta aiwatar da shirin samar da lantarki na shugaban ƙasa tare da kamfanin Siemens.

Ya kuma nemi a ƙarfafa haɗin gwiwa a fannonin makamashi, iskar gas, koyon sana’o’i, fasahar zamani da basirar wucin gadi.

Akpabio ya buƙaci a faɗaɗa haɗin gwiwar tsaro, musayar bayanan sirri da yaƙi da fataucin mutane, tare da samar da hanyoyin ƙaura na halal.

Ya kuma gabatar da shawarar kafa tattaunawar majalisun Najeriya da Jamus akai-akai domin tabbatar da cewa yarjejeniyoyin ƙasashen biyu sun haifar da ayyukan ci gaba da za a iya gani.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *