Shugaban Rundunar Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya halarci bikin shigar da sabbin jirage masu saukar ungulu guda biyar cikin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran manyan jami’an tsaro da gwamnati.
An gudanar da bikin ne ranar Alhamis, 29 ga Oktoba, 2026, inda aka shigar da jirage uku kirar Leonardo AW-109 Trekker B da wasu biyu kirar Airbus H-125 cikin rundunar.
- Manyan ayyukan more rayuwa za su taimaka wa Najeriya cimma tattalin arzikin dala tiriliyan ɗaya – Tinubu
- Shugaba Tinubu ya ce inganta horas da malamai zai bunƙasa ilimin yara a Najeriya
Sabbin jiragen za su taimaka wajen tattara bayanan sirri, sa ido, jigilar jami’an tsaro da kai ɗaukin gaggawa ga sojojin da ke ƙasa, tare da tallafa musu yayin gudanar da ayyukan yaƙi.
Haka kuma, jiragen za su ƙarfafa ayyukan haɗin gwiwa tsakanin rundunonin soji da ƙara musu ƙarfin tunkarar barazanar ta’addanci, fashi da makami da garkuwa da mutane a sassan ƙasar.
Shigar da jiragen cikin rundunar na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin tarayya na sabunta kayan aikin soji da ƙarfafa tsaron ƙasa domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa.