Jam’iyyar ADC ta zargi Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da yin abin da ka iya kawo cikas ga shirye-shiryen zaɓen 2027, tana mai cewa gazawar hukumar ya haifar da shakku kan yiwuwar dage zaɓen.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran jam’iyyar na Ƙasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar ranar 30 ga Oktoba, 2026, jam’iyyar ta ce gano hotunan da aka samar da fasahar AI da kuma bayanan ƙarya a rajistar masu zaɓe ya jefa alamar tambaya ga sahihancin aikin INEC.

ADC ta kuma nuna damuwa kan rashin kama ko gurfanar da jami’an hukumar da ake zargin sun shigar da waɗannan bayanai marasa inganci cikin rajistar, duk da cewa INEC ta amince cewa wasu jami’anta ne suka haddasa matsalar.

Jam’iyyar ta zargi INEC da rashin wallafa rajistar masu zaɓe ta wucin gadi a intanet cikin wa’adin da sashe na 19(1) na Dokar Zaɓe ta 2026 ya tanada, wanda ya ce dole ne a fitar da rajistar domin jama’a su duba ta kafin cikar kwanaki 90 da zaɓe.

Ta kuma yi nuni da cewa sashe na 19(5) ya tanadi hukunci ga jami’in da ya gaza bin wannan doka.

ADC ta buƙaci a gudanar da bincike mai zaman kansa kan rajistar masu zaɓe, a binciki jami’an da ake zargi da hannu cikin kura-kuran, sannan INEC ta yi cikakken bayani kan dalilin rashin bin tanadin dokar.

Ta ce dole ne hukumar ta tabbatar wa ’yan Najeriya cewa za ta bi dokokin zaɓe a duk matakan gudanar da zaɓen 2027.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *