Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta bayyana wasu sharuɗɗan da take buƙatar masu neman aiki a cikinta su cika, ciki har da kasancewa cikin ƙoshin lafiya da bayar da sahihan bayanan shekarunsu.

A cikin saƙon da hukumar ta wallafa, ta ce masu neman aikin dole ne su kasance masu ƙoshin lafiyar jiki, tare da bayyana ainihin shekarunsu ba tare da rage su ba.

Hukumar ta kuma jaddada cewa dole ne masu neman aikin su gabatar da dukkan takardun shaidar karatunsu, tare da tabbatar da cewa sakamakon jarabawar da suka yi nasu ne na gaskiya.

EFCC ta ce masu neman aikin ba za su kasance da tarihin shan miyagun ƙwayoyi ko wasu abubuwan maye ba.

Hukumar ta kuma bayyana cewa horon da za a gudanar na tsawon watanni shida zuwa 12 wajibi ne, kuma ba za a amince wa wanda ya samu gurbin aikin ya ƙi halartar horon ba.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *