Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta kama wasu ’yan Najeriya biyu da ake zargi da safarar hodar iblis zuwa Faransa, bayan an gano sun haɗiye kunshi 200 na ƙwayar a jikinsu a filin jirgin sama na Abuja.
Hukumar ta ce an kama mutanen ne a ranar 28 ga Oktoba, 2026, bayan na’urar tantance jiki ta nuna suna ɗauke da ƙwayar a cikinsu. Daga bisani sun fitar da kunshin hodar iblis ɗin guda 200, waɗanda nauyinsu ya kai kilogram 3.46.
A wani samamen kuma, jami’an NDLEA sun kama wata mata a kan titin Abuja zuwa Kaduna, inda suka ƙwace harsasai 266 na bindigar AK-47 daga hannunta.
- MMPN ta yaba wa Sarkin Musulmi kan shekaru 20 na hidimarsa ga al’umma
- Ba gudu ba ja da baya, za mu ƙaddamar da kamfen a Sakkwato – ADC
Hukumar ta kuma kama wani mutum mai shekaru 68 a kan hanyar Zariya zuwa Kano, tare da kayar ampoules 2,770 na pentazocine, ampoules 100 na diazepam, allunan diazepam 11,000 da kuma allunan Exol-5 guda 4,500.
NDLEA ta ce ta gudanar da wasu samame a jihohin Legas, Oyo, Kano, Kaduna, Ondo, Edo da Sakkwato, inda ta ƙwace miyagun ƙwayoyi da dama tare da lalata gonar wiwi mai girman hekta 1.646.
Shugaban hukumar, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya, ya yaba wa jami’an bisa aikin da suka gudanar.