Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya zargi wasu ’yan hamayya da ƙoƙarin ganin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta cire sunan Aminu Abdussalam Gwarzo daga jerin ’yan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin ƙungiyar matasan Kwankwasiyya a gidansa da ke Miller Road, Kano.
- Sarki Charles zai yi magana kan cinikin bayi a taron ƙasashen Commonwealth
- AAC ta nemi a bayyana yadda aka gano wayar tawagar Sowore kusa da gidan gwamnan Ekiti
Zargin na zuwa ne kwana guda bayan da INEC ta wallafa jerin sunayen ’yan takarar gwamna a shafinta na intanet, ba tare da saka sunan Gwarzo ba.
Sai dai wata majiya daga hukumar INEC ta shaida wa TRT Afrika Hausa cewa batun ba matsalar hukumar ba ce, illa dai yana gaban kotu, kuma za a mayar da sunan Gwarzo cikin jerin idan kotu ta warware matsalar.
Kwankwaso ya ce suna da yaƙinin samun nasara a kotun, yana mai cewa irin wannan lamari ya taɓa faruwa a zaɓen 2019, lokacin da kotu ta tabbatar da takarar Abba Kabir Yusuf kwanaki kaɗan kafin zaɓe, wanda daga bisani suka lashe.