Jamhuriyar Nijar da Libya sun cimma yarjejeniya domin ƙarfafa haɗin gwiwa a wasu muhimman fannoni da suka shafi hulɗar ƙasashen biyu.
An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne yayin ziyarar tawagar Nijar zuwa Libya a ranar Lahadi, inda Firaministan Nijar, Ali Mahamane Lamine Zeine, da Mataimakin Hafsan Hafsoshin Sojojin Libya, Janar Saddam Haftar, suka sanya hannu kan takardun yarjejeniyar.
- Mutane 9 sun mutu a wani hatsarin jirgin sama a Florida
- Mutane 8 sun mutu a hatsarin mota tsakanin Ghana da Burkina Faso
Hakan ya biyo bayan wani zama na musamman da jami’an ƙasashen biyu suka gudanar domin tattauna batutuwan da suka shafi alaƙarsu.
Yarjejeniyar ta zo ne a daidai lokacin da ake samun rahotannin cewa gwamnatin Benghazi ta girke dakaru a kan iyakar Libya da Nijar.
Wasu rahotanni sun danganta matakin da zargin ƙoƙarin dakile yiwuwar girke sojojin Aljeriya a Nijar domin kare muradunta, sai dai ba a tabbatar da wannan alaƙa ba.