Hukumar Kula da Rajistar Shaidar Ɗan Ƙasa ta Najeriya (NIMC) ta kama wasu mutane da ake zargi da gudanar da rajistar lambar shaidar ɗan ƙasa ta NIN ba bisa ƙa’ida ba a Gwagwalada da wasu wurare, yayin da take ƙara ƙaimi wajen yaƙi da cibiyoyin rajista marasa izini, sauya bayanan mutane ba bisa ƙa’ida ba da karɓar kuɗaɗen haram.

A cikin wata sanarwa da Shugaban Sashen Hulɗa da Jama’a na hukumar, Kayode Adegoke, ya fitar, ya ce sashen sa ido kan bin ƙa’idoji da aiwatar da doka na NIMC ya kuma ƙwace wasu kayan aiki da ake zargin waɗanda aka kama suna amfani da su.

Sanarwar ta ce Darakta-Janar ta hukumar, Abisoye Coker-Odusote, ta jaddada cewa NIMC ba za ta lamunci karɓar kuɗaɗen haram ko wasu munanan ayyuka daga ma’aikata da masu gudanar da rajista ba.

Hukumar ta kuma bayyana cewa dole ne a gudanar da rajistar NIN a cibiyoyin da ta amince da su kawai, yayin da duk wani buƙatar gyara bayanan mutum ya kamata a bi ta dandalin gyaran bayanai na hukumar da aka amince da shi.

NIMC ta shawarci masu lambar NIN da su riƙa amfani da hanyoyin da hukumar ta amince da su, tare da sauke manhajar NINAuth, wadda ke da wasu ƙarin matakan tsaro da suka haɗa da kare lambar NIN da kuma ba da damar buga takardar shaidar NIN.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *