Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya zargi gwamnatin jihar da tauye ’yancin siyasar ’yan adawa, yana mai cewa ba za su amince da duk wani yunƙuri na hana ’yan Najeriya gudanar da harkokinsu na siyasa ba.

Tambuwal ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar baƙuncin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar SDP, Prince Adewole Adebayo, wanda ya kai masa ziyarar ban girma a Sakkwato.

A yayin ziyarar, Adebayo ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta mutunta bambancin ra’ayin siyasa tare da tabbatar da ’yancin zirga-zirgar ’yan adawa.

Tsohon gwamnan ya yi zargin cewa an rufe ofishin kamfen na jam’iyyar ADC a jihar, sannan jami’an wasu rundunonin tsaro da gwamnati ta amince da su, ciki har da Sokoto Marshal da Community Guards, sun kai hari kan ɗan takarar gwamnan ADC, Manir Muhammad Dan’iya.

Ya ce irin waɗannan abubuwa ba su dace da tarihin Sakkwato na zaman lafiya, karɓar baƙi da mutunta bambancin ra’ayin siyasa ba.

Tambuwal ya jaddada cewa jihar mallakar dukkan ’yan Najeriya ce, don haka ya kamata kowa ya samu damar zuwa cikinta da gudanar da harkokinsa ba tare da la’akari da jam’iyyar da yake goyon baya ba.

A nasa jawabin, Adebayo ya ce ya ziyarci jihar ne domin taya Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na III, murnar cika shekaru 20 da hawa karagar mulki.

Ya bayyana Sakkwato a matsayin muhimmiyar cibiyar tarihi, ilimi da siyasar Najeriya, tare da jaddada cewa bai kamata a hana kowane ɗan Najeriya shiga wani yanki na ƙasar saboda bambancin ra’ayin siyasa ba.

Tambuwal ya kuma yaba wa Adebayo bisa jarumtaka da kishin ƙasa, tare da bayyana shirinsa na yin aiki tare da shi domin ci gaban Najeriya ko da wane ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *