Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya karrama Shugaban Ƙungiyar JIBWIS ta Ƙasa, Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, da lambar yabo ta musamman mai suna Sheikh Abdullahi Fodiyo Exemplary Prize for Knowledge and Scholarship ta shekarar 1448AH/2026.

An bai wa Sheikh Bala Lau lambar yabon ne bisa gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa ilimi, hidimtawa addinin Musulunci da yaɗa koyarwar Sunnah ta Annabi Muhammad (SAW).

A cikin wasiƙar sanar da karramawar, Sarkin Musulmi ya bayyana cewa an zaɓi shugaban JIBWIS ɗin ne bayan nazari da shawarwari kan gudunmawar da ya bayar da kuma sadaukarwarsa wajen yaɗa ilimi da kyawawan koyarwar Musulunci.

An miƙa masa lambar yabon ne ranar Litinin, 2 ga Nuwamba, 2026, a matsayin girmamawa ga ayyukan da ya gudanar a fannin ilimi da addini.

Sarkin Musulmi ya yi addu’ar Allah Ya karɓi ayyukan Sheikh Bala Lau a matsayin ibada, Ya ƙara masa lafiya da tsawon rai, tare da ba shi ikon ci gaba da hidimtawa al’ummar Musulmi.

Babban Sakataren JIBWIS na Ƙasa, Sheikh Dr. Muhammad Kabir Haruna Gombe, da Alaramma Nasiru Salihu Gwandu na cikin waɗanda suka raka shugaban ƙungiyar zuwa wajen taron karɓar lambar yabon.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *