Kamfanin NNPC Limited ya gabatar da wani bincike kan amfani da fasahar koyon na’ura (Machine Learning) wajen tantance yiwuwar samun albarkatun mai da iskar gas a yankunan da ba a gudanar da cikakken binciken mai ba.

NNPC ta gabatar da binciken ne a ranar Talata, yayin taron ƙasa da ƙasa kan harkokin man fetur na ADIPEC 2026 da ke gudana a Abu Dhabi, cikin shirin gabatar da takardun bincike na ƙungiyar SPE.

Binciken mai taken Petroleum Target Explorer (PTX-AIM), ya yi nazari kan yadda za a yi amfani da fasahar koyon na’ura wajen hasashen yawan sinadarin Total Organic Carbon (TOC) da ke cikin duwatsun da ke samar da mai da iskar gas, tare da amfani da rijiyar Kolmani River-2 da ke yankin Gongola Basin a matsayin misali.

Dokta Fodio Longman, mai bincike a sashen NNPC Research, Technology & Innovation, ne ya gabatar da takardar, tare da haɗin gwiwar Husaini Balarabe da Ifeanyichukwu Edeh.

Longman ya bayyana cewa tantance yawan sinadarin TOC a yankunan da ba a yi wa cikakken bincike ba na da wahala saboda ƙarancin bayanan gwaje-gwajen dakunan bincike, da kuma bambance-bambancen yanayin ƙasa da ingancin bayanan da ake da su.

Da yake tsokaci kan binciken, babban jami’in kirkire-kirkire na NNPC RTI, Rasheed Ojulari, ya ce aikin na nuna bunƙasar ƙwarewar bincike ta sashen, da yadda ake amfani da fasahar koyon na’ura wajen nazarin tsarin samuwar mai, domin taimaka wa Najeriya wajen ƙara yawan arzikin man fetur da iskar gas cikin rahusa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *