Rundunar sojojin ta ce dakarunta na runduna ta 12, tare da haɗin gwiwar jami’an hukumar tsaron sa-kai ta Jihar Kogi, sun kai samamen ne a ranar 4 ga Nuwamba, 2026, yayin ci gaba da samame kan waɗanda ake zargi da garkuwa da mutane a yankin.
A cewar sanarwar, jami’an tsaron sun faɗaɗa bincikensu daga dajin Edimogbo zuwa yankin dajin Obele, domin bin sawun waɗanda ake zargin da suka tsere bayan samamen farko.
- NDLEA ta taya sabon kwamishinan tsaron cikin gida na Kano murna
- Hakeem Baba-Ahmed ya ce zaɓukan Amurka darasi ne ga shugabannin Najeriya
A yayin samamen, sun yi arba da waɗanda ake zargin, waɗanda suka yi ƙoƙarin tserewa bayan hango jami’an tsaro, lamarin da ya kai ga kashe uku daga cikinsu.
Bayan fafatawar, dakarun sun ƙwato bindigogi huɗu ƙirar AK-47, alburusai 336 masu girman 7.62mm, bandolier guda uku da kuma katin shaida.
Kwamandan runduna ta 12 Composite Brigade, Birgediya-Janar Kasim Umar Sidi, ya yaba wa sojojin da jami’an hukumar tsaron sa-kai bisa jajircewarsu da ƙwarewarsu, tare da buƙatarsu da su ci gaba da matsa lamba kan masu aikata laifuka a yankin.
Rundunar sojin ta tabbatar wa al’ummar Kogi da kewaye cewa za ta ci gaba da ƙoƙarin kare rayuka da dukiyoyi, tare da kira ga jama’a da su riƙa bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai a kan lokaci domin taimaka wa ayyukan da suke gudanarwa.