Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya karɓi tawagar shugabannin Ƙungiyar Musulman Kudu maso Yammacin Najeriya (MUSWEN), waɗanda suka kai masa ziyarar ban girma a gidan gwamnatin Legas da ke Marina.

Sanwo-Olu ya bayyana cewa sun tattauna muhimmiyar rawar da shugabannin addinai za su taka wajen inganta zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna tsakanin al’ummomi.

Gwamnan ya bayyana jin daɗinsa kan gudummawar da shugabannin addinai ke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da kyakkyawar mu’amala a cikin al’umma.

Ya kuma yaba wa MUSWEN da sauran shugabannin addinai bisa haɗin gwiwar da suke ci gaba da bai wa gwamnatinsa wajen gina Jihar Legas mai haɗa kowa da kowa, tare da tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *