Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta kori shugabancin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark, tare da soke duk matakan da shugabancin ya ɗauka a madadin jam’iyyar, ciki har da zaɓen tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Mai shari’a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis, inda ya bayyana kwamitin riƙon ƙwarya da Mark ke jagoranta a matsayin wanda bai samu halaccin shugabancin jam’iyyar ba.
Kwamitin ne ya shirya zaɓen fidda gwani da ya samar da Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC.
- APC ta ce gwamnatin Tinubu ta bayar da rancen karatu na Naira biliyan 372.62bn, tare da horas da matasa 156,446
- Obi ya yi alƙawarin farfaɗo da tashar jiragen ruwa ta Calabar da yawon buɗe ido a Cross River
Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na shiyyar Arewa maso Gabas, Nafiu Bala Gombe, ya shigar domin ƙalubalantar yadda kwamitin Mark ya karɓi ragamar shugabancin jam’iyyar.
Gombe ya ce bayan murabus ɗin tsohon shugaban jam’iyyar, Ralph Nwosu, shi ne ya kamata ya karɓi shugabancin bisa tanadin kundin tsarin jam’iyyar.
A ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1819/2025, Gombe ya nemi kotu ta soke matakan da shugabancin Mark ya ɗauka, tare da hana Mark da Rauf Aregbesola gabatar da kansu a matsayin shugaban ADC na ƙasa da sakatarenta.
Kotun ta amince da buƙatunsa, lamarin da ya shafi sahihancin zaɓen fidda gwani da ya samar da Atiku a matsayin ɗan takarar jam’iyyar, duk da cewa hukumar INEC ta riga ta wallafa sunansa.
Sai dai jami’in jin daɗin mambobin ADC na ƙasa, Nkemakolam Ukandu, ya ce jam’iyyar za ta ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin.
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan Atiku ya gudanar da babban gangamin kamfen a Jihar Sakkwato, a wani ɓangare na shirye-shiryensa na neman shugabancin ƙasar a 2027.