Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi alƙawarin farfaɗo da tashar jiragen ruwa ta Calabar tare da dawo da martabar Jihar Cross River a fannin yawon buɗe ido idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa.
Obi ya bayyana hakan ne yayin taron tattaunawa da al’ummar jihar a Calabar ranar 4 ga Nuwamba, 2026.
Kafin taron, Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso sun jagoranci ’yan takarar NDC na jihar da sauran mambobin jam’iyyar zuwa fadar Obong na Calabar, Edidem Ekpo Okon Abasi Otu V, domin gaisuwa.
A yayin taron, mahalarta sun yi tambayoyi kan shirye-shiryen jam’iyyar game da tashar jiragen ruwa ta Calabar, tsaro, tattalin arziki, yawon buɗe ido da kuma walwalar al’umma.
- APC ta ce gwamnatin Tinubu ta bayar da rancen karatu na Naira biliyan 372.62bn, tare da horas da matasa 156,446
- Bill Clinton ya buƙaci Democrat su mayar da hankali kan rage tsadar rayuwa bayan nasarar zaɓe
Obi ya ce shi da Kwankwaso sun kuduri aniyar haɗa kan ƙasar da tabbatar da tsaro, tare da zuba jari mai yawa a fannoni kamar ilimi da kiwon lafiya domin rage talauci.
Ya kuma yi alƙawarin cewa idan suka samu nasara, za su tabbatar da tashar jiragen ruwa ta Calabar ta fara aiki yadda ya kamata, tare da sauran tashoshin jiragen ruwa da ke yankin Neja Delta.
Dangane da yawon buɗe ido, Obi ya ce Calabar, Obudu da sauran wurare a Cross River sun taɓa kasancewa cikin wuraren da ’yan Najeriya da baƙi ke ziyarta, amma a cewarsa, rashin kyakkyawan shugabanci da kulawa sun rage martabarsu.
Ya yi alƙawarin farfaɗo da fannin, har ma ya ce zai riƙa gudanar da hutunsa a wuraren yawon buɗe ido na jihar idan ya zama shugaban ƙasa.
Obi ya kuma buƙaci mambobi da magoya bayan jam’iyyar su kasance cikin shiri domin kare ƙuri’unsu a ranar zaɓe, yana mai godiya ga waɗanda suka halarci taron da kuma al’ummar Cross River bisa kyakkyawar tarba da suka yi musu.