Tsohon shugaban ƙasar Amurka, Bill Clinton, ya taya ’yan takarar jam’iyyar Democrat da suka samu nasara a zaɓen tsakiyar wa’adin shekarar 2026 murna, tare da gode wa waɗanda suka taimaka wajen ganin sun yi nasara.
A cikin sanarwar da ya fitar ranar 4 ga Nuwamba, Clinton ya ce ’yan takarar da aka zaɓa sun nuna bambancin al’ummar Amurka da ƙarfin jam’iyyar Democrat.
Ya ce sakamakon zaɓen ya nuna cewa al’ummar Amurka na son a mayar da hankali kan bukatunsu maimakon abin da ya kira rikice-rikice da rashawa daga Washington.
- Sarkin Musulmi ya karɓi baƙuncin Atiku Abubakar a fadarsa da ke Sakkwato
- Sarkin Gaya ya dakatar da Dagacin Shagogo bisa zargin rashin da’a
Ya lissafa rage tsadar rayuwa, kare harkokin kiwon lafiya, kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe marasa ma’ana da harajin shigo da kaya da ke ƙara tsadar kayayyaki a matsayin muhimman abubuwan da ya kamata a magance.
Clinton ya kuma jaddada buƙatar shawo kan bashin ƙasar da kuma tabbatar da cewa waɗanda ke kan madafun iko sun ɗauki alhakin ayyukansu a gaban al’ummar da suke yi wa hidima.
Ya ce nasarar da jam’iyyar ta samu ta ba ta dama da kuma nauyin da ke kanta na sake gina amincewar jama’a, yana mai kira ga ’yan Democrat da su gudanar da hakan cikin tawali’u da ƙuduri, tare da buɗe ƙofa ga waɗanda ba su zaɓe su ba.
A ƙarshe, Clinton ya ce Amurkawa sun sake ba jam’iyyar damar tabbatar da cewa haɗin kai na taimaka wa ƙasa, yana mai kira ga ’yan jam’iyyar da su yi amfani da wannan dama yadda ya kamata.