Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya karɓi ziyarar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, a fadarsa da ke Sakkwato.
Atiku ya kai ziyarar ne a daren ranar Laraba, 5 ga Nuwamba, 2026, tare da wasu mambobin tawagarsa, inda Sarkin Musulmi ya tarbe su tare da nuna jin daɗinsa bisa ziyarar.
A yayin ganawar, Sarkin Musulmi ya jaddada muhimmancin zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna wajen magance matsalolin da Najeriya ke fuskanta, tare da bayyana rawar da sarakunan gargajiya ke takawa wajen inganta zaman tare da ci gaban ƙasa.
- Atiku ya yi alƙawarin buɗe iyakokin Najeriya idan ya ci zaɓen 2027
- Musulmai takwas za su wakilci al’ummarsu a Majalisar Dokokin Amurka – Ilhan Omar
A nasa jawabin, Atiku Abubakar ya gode wa Sarkin Musulmi bisa kyakkyawar tarba da karimcin da ya nuna masa da tawagarsa, tare da yaba rawar da sarakunan gargajiya ke takawa wajen samar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.
Ziyarar ta ba su damar tattauna batutuwan da suka shafi ƙasa, da kuma hanyoyin ƙarfafa zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba.
Sarkin Musulmi ya samu rakiyar Wazirin Sakkwato da sauran manyan fadawa, da kuma Sakataren Majalisar Masarautar Sakkwato.