Yar’ majalisar wakilan Amurka Ilhan Omar ta taya Abdul El-Sayed murna, ta ce Musulmi takwas za su wakilci al’ummarsu a Majalisar Dokokin Amurka.
A cikin saƙon taya murnar, Ilhan Omar ta ce: “Abdul El-Sayed, ina taya ka murna. Ka mayar da addu’ar ‘Insha Allah’ zuwa ‘Alhamdulillah’.”
- Atiku ya yi alƙawarin buɗe iyakokin Najeriya idan ya ci zaɓen 2027
- Gwamnan Edo da Sarkin Benin sun goyi bayan yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi
Ta bayyana cewa ta cika da godiya da sanin cewa yanzu Musulmi takwas za su kasance cikin waɗanda ke aiki a Majalisar Dokokin Amurka.
Ilhan Omar ta ce a baya an gaya musu cewa ba za su iya bayyana ra’ayoyinsu ba, ƙalubalantar tsarin da ake ciki ko kaiwa wannan matsayi, amma sun samu nasarar yin hakan.
Ta kammala saƙon da kalmar “Alhamdulillah”, wato godiya ga Allah.