Hukumar Kwastam ta Najeriya ta fara wayar da kan masu ruwa da tsaki kan sabon tsarin tantancewa da amincewa da fitar da kayan da suka daɗe a tashar jiragen ruwa ta Apapa, domin magance matsalolin da ke tattare da tsarin takardun hannu.

Kwamandan Kwastam mai kula da shiyyar Apapa, Comptroller Murtala Mu’azu, ne ya jagoranci shirin wayar da kan jama’a da aka gudanar a ranar Talata, 3 ga Nuwamba, 2026, wanda ya haɗa da manyan jami’an hukumar, masu karɓar kaya da sauran masu gudanar da ayyukan tashar.

Mu’azu ya ce tsohon tsarin takardun hannu na ɗaukar lokaci mai tsawo kafin a samu amincewar ƙarshe, lamarin da ke haifar da tsaiko da rikice-rikice a harkokin cinikayya.

Ya bayyana cewa ana tantance tsawon lokacin da kaya suka shafe a tashar tare da aika rahotanni zuwa hedikwata ne da hannu, wanda ke haifar da gibi tsakanin tattara bayanai da yanke hukunci.

Kwamandan ya ce sabon tsarin na zamani zai kawar da maimaita aika takardu da kuma jinkirin tattara bayanai, tare da sauƙaƙa tantance matakin amincewar da ya dace da kowane kaya.

Ya bayar da misalin yadda kaya da suka shafe kwanaki 31 ko 32 a tashar kan iya shiga wani sabon mataki kafin hedikwata ta yanke hukunci kan rahoton da aka aika mata, wanda ke haifar da matsala wajen tantance matakin da ya dace a bi.

Mu’azu ya ce shirin wayar da kan jama’a zai taimaka wa jami’an Kwastam wajen samun cikakken ilimi kan tantancewa da amincewa da buƙatun fitar da kayan da suka daɗe a tashar, yana mai cewa jami’an fasahar sadarwa da masu horaswa za su ci gaba da ba da taimakon fasaha ga masu amfani da tsarin.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *