Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta gudanar da horo na musamman ga jami’an horas da ma’aikatan zaɓe daga jihohi, domin shirya su tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Cibiyar Horas da Ma’aikatan Zaɓe ta hukumar ce ta shirya taron na kwanaki huɗu, wanda aka gudanar daga ranar Talata 3 zuwa Juma’a 6 ga Nuwamba, 2026, a otal ɗin Ajuji Greenwich da ke Gudu, Abuja.

Taron ya haɗa da jami’an horas da ma’aikatan zaɓe na jihohi da mataimakansu, inda aka tsara ba su ƙwarewar aiki, ilimi da fahimtar tsarin zaɓe da kuma buƙatun gudanar da horas da jami’an zaɓe yadda ya kamata.

Kwamishinan INEC na ƙasa, kuma mamba a hukumar gudanarwar Cibiyar Horas da Ma’aikatan Zaɓe, Farfesa Sunday Ajah, ne ya buɗe taron.

Ya ce hukumar na dogaro da ƙwarewa, jajircewa da kishin aikin mahalarta wajen tabbatar da cewa an gudanar da dukkan shirye-shiryen horaswa yadda ya kamata, sannan kowane jami’in zaɓe ya samu shirin da ya dace kafin gudanar da aikinsa a zaɓen 2027.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *