Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta buƙaci maniyyatan aikin Hajjin 2027 da sauran jama’a su riƙa bibiyar shafukanta na sada zumunta domin samun sahihan bayanai da sanarwa kan shirye-shiryen aikin Hajjin.
Hukumar ta ce za ta riƙa amfani da waɗannan kafafe wajen sanar da jama’a ayyukanta, shirye-shiryen Hajji da kuma jagororin da suka shafi aikin ibadar.
- An kashe mutum biyu, an sace wasu 20 a harin ‘yan bindiga a Kaduna
- Gwamnati Tarayya ta amince da zuba jarin dala miliyan 105 a masana’antar kirkire-kirkire ta Afirka
NAHCON ta kuma ƙarfafa wa jama’a gwiwar bin shafukanta na hukuma, tare da yin alama ta so da kuma rajista domin samun bayanai a kai a kai.
Hukumar ta bayyana cewa matakin na da nufin tabbatar da cewa maniyyata da sauran jama’a sun samu sahihan bayanai daga majiyarta kai tsaye, tare da kasancewa cikin masaniya kan shirye-shiryen Hajjin 2027.