Majalisar Wakilan Najeriya ta yi watsi da ƙorafin da ya nemi soke lasisin rarraba iskar gas da aka bai wa kamfanin NIPCO Plc a wasu yankunan ƙasar.
Ƙungiyar Nigerian Energy Security Watch Group ce ta shigar da ƙorafin, inda ta ƙalubalanci lasisin da Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur ta Tsakiya da Ƙasa (NMDPRA) ta bayar domin gudanar da harkokin rarraba iskar gas a jihohin Legas, Ogun, Oyo da Osun, da kuma yankin Lekki Free Trade Zone.
- Idris ya buƙaci kwamishinonin APC su yaƙi bayanan ƙarya, su saurari koke-koken jama’a
- An kashe mutum biyu, an sace wasu 20 a harin ‘yan bindiga a Kaduna
Kwamitin bincike na musamman ƙarƙashin kwamitin majalisar mai kula da harkokin man fetur na ɓangaren kasuwanci, wanda ɗan majalisa Peter Aniekwe ke jagoranta, ya ce ƙungiyar ba ta gabatar da hujjojin da za su tabbatar da zargin da ta yi ba.
Kwamitin ya bayyana ƙorafin a matsayin wanda aka gina bisa jita-jita kuma ba shi da isasshen tushe, bayan gudanar da bincike kan batun.
Ya kuma jaddada cewa bayar da lasisin irin wannan aiki na cikin hurumin doka na hukumar NMDPRA ƙarƙashin Dokar Masana’antar Man Fetur ta 2021 (Petroleum Industry Act), yayin da majalisar za ta ci gaba da sa ido kan ayyukan hukumomin domin kare muradun jama’a.