Gwamnatin Tarayya da abokan hulɗarta sun sake jaddada aniyarsu ta ƙara zuba jari a masana’antar kirkire-kirkire domin mayar da basirar ’yan Afirka zuwa arziki, samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziki.

An bayyana hakan ne yayin buɗe taron Creative Africa Nexus Weekend (CANEX WKND) 2026 da aka gudanar a Legas, inda gwamnatin Najeriya ta tabbatar da aniyarta ta gina masana’antar kirkire-kirkire mai ƙarfi da za ta taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

Rahoton gidan talabijin NTA ya bayyana cewa masana’antar na fuskantar ƙalubale da suka haɗa da ƙarancin hanyoyin samun kuɗaɗen jari, rashin isassun kayayyakin more rayuwa da wahalar shiga kasuwannin duniya, duk da irin basirar da ake da ita a nahiyar Afirka.

Rahoton ya kuma bayyana cewa an riga an kulla yarjejeniyoyin zuba jari da suka kai dala miliyan 105, duk da cewa ba a fayyace sunayen waɗanda suka sanya hannu kan yarjejeniyoyin ko fannoni da za a zuba jarin a cikinsu ba.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *