Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, da mataimakinsa, Kashim Shettima, sun isa birnin Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom, domin halartar gangamin kamfen na jam’iyyar APC.
- Kwamandan sojojin Senegal ya gana da dakarun Najeriya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Gambia
- Amnesty International ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wa ayarin motocin ADC a Kebbi
Shugaban da mataimakinsa sun samu tarba daga Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno, da shugabannin jam’iyyar da dubban magoya baya da suka taru domin halartar gangamin.
Hakan na cikin shirye-shiryen jam’iyyar APC na yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa.