Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta yi Allah-wadai da hare-haren da aka kai wa ayarin motocin kamfen na jam’iyyar ADC a Jihar Kebbi ranar Alhamis.

Ƙungiyar ta ce bidiyoyin da ta tantance sun nuna wasu mutane dauke da makamai suna kai wa ayarin motocin hari, tare da dukan mutane da sanduna da adduna da kuma tare hanyoyi.

Amnesty ta ce a wani bidiyo daga Argungu, an ga yadda wasu ’yan daba suka far wa magoya bayan jam’iyyar, suka yi musu duka tare da lalata motocinsu.

Ta kuma ce an jefi motocin da kwalabe da duwatsu, tare da lalata kyamarori da sauran kayan aikin ’yan jarida.

Ƙungiyar ta bayyana cewa irin waɗannan hare-hare na tauye ’yancin ’yan adawa da magoya bayansu na yin taro da kafa ƙungiyoyi cikin lumana. Ta ƙara da cewa harin Kebbi ya biyo bayan makamancin abin da ya faru a Jihar Sakkwato.

Amnesty International ta zargi hukumomin Najeriya da gaza kare al’umma da hukunta waɗanda ke da hannu a hare-haren da ta ce sun faru a jihohin Neja, Kaduna, Edo da Enugu.

Ta yi kira ga gwamnatin tarayya, rundunar ’yan sanda da hukumar DSS da su ɗauki matakan dakile hare-haren tare da tabbatar da adalci ga waɗanda abin ya shafa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *