Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 11 da ke Bompai ta yanke wa Umar Auwal da Yakubu Dayyabu hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samunsu da laifin kashe Fatima Abubakar da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi Ciranci.

Mai Shari’a Nasiru Saminu ne ya yanke hukuncin a ranar Juma’a, 6 ga Nuwamba, 2026, bayan nazarin shaidu da hujjojin da aka gabatar a gaban kotun.

Kotun ta samu Umar Auwal, wanda aka fi sani da Breaker, da Yakubu Dayyabu, wanda ake kira Wawo, da laifin kisan da ya faru ranar 17 ga Janairu, 2026.

Sai dai kotun ba ta samu Isiyaku Yakubu da laifi ba a wannan shari’ar. Duk da haka, ta ce a ci gaba da tsare shi har zuwa ranar 11 ga watan Nuwamba, domin yanke hukuncin ƙarshe kan zargin kisan wata matar aure da kishiyarta a unguwar Tudun Yola, kamar yadda jaridar Arewa Update ta ruwaito

Tawagar masu gabatar da ƙara ta ƙunshi Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabir Maude, tare da Barrister Salisu Muhammad Tahir. Barrister J. I. Musa da Barrister A. I. Baba ne suka wakilci waɗanda ake ƙara.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *