Shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), Birgediya Janar MB Marwa (mai ritaya), ya gabatar da lacca kan yaƙi da shaye-shaye da amfani da miyagun ƙwayoyi a rundunar sojin Najeriya.
Marwa ya gabatar da laccar ne a taron kwamandojin rundunar sojin Najeriya na RSM karo na biyu na shekarar 2026, wanda aka gudanar a ranar Juma’a, 6 ga Nuwamba, a birnin Benin da ke Jihar Edo.
- Kano: Kotu ta yanke wa mutum biyu hukuncin kisa kan kashe uwa da ’ya’yanta shida
- Hukumar NMDPRA ta ce Najeriya na buƙatar jarin dala biliyan 50 domin bunƙasa iskar gas zuwa 2030
Taken laccar shi ne rawar da manyan jami’an RSM za su taka wajen hana shaye-shaye, gano matsalar tun da wuri da kuma taimaka wa waɗanda abin ya shafa wajen samun kulawar da ta dace.
Taron ya samu halartar babban hafsan sojin Najeriya, Laftanar Janar Wahab Shaibu, da manyan jami’an NDLEA, da sauran manyan baƙi da jami’ai da sojojin Najeriya.