Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya taya tawagar ƙwallon ƙafar mata ta ƙasa ’yan ƙasa da shekara 17, Flamingos, murnar lashe Kofin Duniya bayan doke Japan da ci 2-1 a wasan ƙarshe.
Atiku, wanda ya bayyana hakan a matsayin nasarar tarihi, ya ce ƙungiyar ta ba Najeriya farin ciki da alfahari ta hanyar lashe kofin FIFA na farko a wannan mataki na gasar mata ’yan ƙasa da shekara 17.
- Najeriya ta lashe Gasar Cin Kofin Duniya bayan doke Japan 2-1
- Tinubu ya taya Flamingos murnar lashe Kofin Duniya, ya ce sun ɗaukaka martabar Najeriya da Afirka
Ya bayyana cewa kyaftin ɗin tawagar, Harmony Chidi, ta taɓa bayyana burinta na ganin ta yi abin da zai faranta wa takwarorinta da ƙasarta rai, yana mai cewa yanzu wannan buri ya zama abin alfahari ga dukkan ’yan Najeriya.
Tsohon mataimakin shugaban ya yaba wa kyaftin ɗin, sauran ’yan wasa, mai horas da su, Akeem Busari, da dukkan ma’aikatan fasaha da masu taimaka wa ƙungiyar bisa gudummawar da suka bayar wajen samun nasarar.
Atiku ya ce ’yan matan sun nuna irin nasarorin da matasan Najeriya za su iya cimmawa idan aka ba su kulawa da damar bunƙasa hazakarsu, yana mai fatan nasarar za ta ƙarfafa sauran ’yan mata su rungumi burinsu da ƙarfin gwiwa.