Tawagar matan Najeriya ta ‘yan kasa da shekaru 17, wato Flamingos, ta kafa tarihi bayan doke Japan da ci 2-1 a wasan karshe na Gasar Cin Kofin Duniya ta mata ta FIFA ‘yan kasa da shekaru 17 ta shekarar 2026, da aka gudanar a birnin Rabat na kasar Marokko.

Wannan shi ne karon farko da Najeriya ta kai wasan karshe na gasar, inda ‘yan wasan suka nuna bajinta da kwarewa wajen taka leda, lamarin da ya sa suka zama tawaga ta farko daga nahiyar Afirka da ta lashe wannan gasa.

Awawu Bashiru ce ta fara jefa kwallo a ragar Japan, kafin Oluebube Umejiaku ta kara ta biyu a farkon rabin lokaci na biyu, inda ta bai wa Flamingos damar tafiyar da wasan.

An buga wasan ne a filin wasa na Mohammed VI Football Academy, Pitch 3, da ke garin Salé na kasar Morocco.

Sai dai Japan ta rage tazarar kwallayen a minti na 80, bayan da Fuki Ito ta zura kwallo a raga, amma ‘yan wasan Najeriya sun yi nasarar kare ragarsu har zuwa busar karshe, inda suka samu gagarumar nasara.

Wannan nasara ta kuma kammala gagarumin sauyi da tawagar koci Akeem Busari ta samu a gasar, bayan da ta fara fafatawarta da rashin nasara a hannun Poland, kafin daga bisani ta yi nasarar lashe wasanni shida a jere har ta dauki kofin gasar.

Wannan nasara ta zama wani babban tarihi a kwallon kafar mata ta Najeriya, kasancewar wannan ne karon farko da Flamingos ta lashe kofin duniya na mata ‘yan kasa da shekara 17.

Yadda Najeriya ta kai wasan karshe

Najeriya ta samu tikitin zuwa wasan karshe ne bayan wata tafiya mai cike da kalubale da nasarori.

Bayan shan kashi da ci 2-1 a hannun Poland a wasansu na farko, tawagar ta farfado, inda ta samu nasarori a kan Puerto Rico, da Koriya ta Arewa mai rike da kofin gasar, da Mexico, da Venezuela da kuma Brazil.

A wasan kusa da na karshe, Najeriya ta doke Brazil da ci 3-1, inda Queen Joseph ta taka muhimmiyar rawa, yayin da Bashiru ta zura kwallaye biyu, abin da ya tabbatar wa Najeriya gurbin zuwa wasan karshe a karon farko.

A bangare guda, Japan ta samu damar zuwa wasan karshe ne bayan wata gagarumar fafatawa da Koriya ta Arewa a wasan kusa da na karshe, inda ta farke kwallayen da aka zura mata, kafin daga bisani ta yi nasarar tsallakewa ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron raga wato fenareti.

Wannan nasara ta zama wani muhimmin tarihi ga tawagar Flamingos, tare da kafa sabon tarihi a tarihin kwallon kafar matan nahiyar Afirka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *