Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya tawagar ƙwallon ƙafar mata ta ƙasa ‘yan ƙasa da shekara 17, wato Flamingos, murnar lashe Kofin Duniya na FIFA na mata ‘yan ƙasa da shekara 17, bayan doke Japan da ci 2-1 a wasan ƙarshe da aka gudanar a ƙasar Maroko.

Tinubu ya bayyana farin cikinsa ne bayan dawowarsa daga ziyarar aiki a jihohin Akwa Ibom da Rivers, inda ya tarar da uwargidansa, Oluremi Tinubu, na kallon wasan ƙarshe da aka fafata tsakanin Najeriya da Japan.

A cikin saƙon taya murnar, shugaban ya ce nasarar ta bai wa Najeriya da nahiyar Afirka ɗaukaka, domin Flamingos ta zama ƙungiyar farko daga Afirka da ta lashe kofin tun bayan fara gasar.

Ya ce ya bibiyi yadda tawagar ta gudanar da wasanninta a gasar, yana mai tunawa da alkawarin da ’yan wasan suka yi na dawo da kofin gida bayan nasarar da suka samu a wasan kusa da na ƙarshe.

Ya ce sun cika wannan alƙawari ta hanyar jajircewa, ladabi da amincewa da ƙarfinsu.

Tinubu ya bayyana cewa nasarar ta wuce harkar ƙwallon ƙafa, domin za ta ƙarfafa gwiwar miliyoyin ’yan mata a Najeriya su yi manyan buri, su fafata da ƙwararru kuma su kai ga cimma burinsu a fannoni daban-daban.

Ya taya ’yan wasan, masu horas da su, Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF), Hukumar Wasanni ta Ƙasa da duk waɗanda suka taimaka wajen wannan nasara murna, yana mai cewa a madadin gwamnati da al’ummar Najeriya, yana gaishe da sabbin zakarun duniya.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *