Rundunar ’yan sandan Najeriya ta kama wata mata bisa zargin ba wa wasu yara biyu wani abu da ake zargin guba ne a yankin Takuti, Ƙaramar Hukumar Lapai ta Jihar Neja.
Rundunar ta ce lamarin ya faru ne a ranar 6 ga Nuwamba, 2026, kuma ɗaya daga cikin yaran, mai shekara tara, ta rasu.
- Kamfanin siminti na Dangote ya tallafa wa ’yan kasuwa 15 a Kogi
- NDLEA ta kama ’yar Uganda da hodar iblis 87 a al’aurarta
Yarinyar ta biyu mai shekara huɗu kuma an garzaya da ita Babban Asibitin Lapai, inda rundunar ta ce tana samun sauƙi a lokacin fitar da sanarwar.
Bayan faruwar lamarin, jami’an ’yan sanda sun kama matar da ake zargi, wadda take tsare a hannun rundunar.
Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike domin gano yadda lamarin ya faru da kuma tabbatar da abin da ya jawo mutuwar ɗaya daga cikin yaran.