Rundunar ’yan sandan Najeriya ta kama wani matashi mai shekara 22 da ake zargi da hannu wajen sace wani yaro mai shekara tara, Ubaidu Sammani, a Jihar Kano.

Sanarwar rundunar ta ce an kama wanda ake zargin, wanda aka fi sani da Sankolo, a unguwar Rimin Kebe a ranar 6 ga Nuwamba, 2026.

Ana zargin matashin da hannu wajen sace yaron a ranar 3 ga Yuli, 2026, kuma rundunar ta ce tana ƙoƙarin gano inda aka ɓoye shi domin ceto shi.

Haka kuma, rundunar ta ce tana ƙoƙarin cafke sauran waɗanda ake zargin suna da hannu a lamarin.

Wanda ake zargin yana hannun ’yan sanda, yayin da bincike ke ci gaba.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *