Hukumar Kwastam ta Najeriya ta ce ta tara kuɗaɗen shiga har Naira tiriliyan 1.42 cikin watanni biyu, daga watan Satumba zuwa Oktoba na shekarar 2026.

Kakakin hukumar, Abdullahi Maiwada, ya bayyana cewa an samu kuɗaɗen ne bayan sarrafa rahotannin tantance kaya 9,195 kafin isowarsu ƙasar, tare da takardun sanar da kaya guda 99,839.

Ya ce nasarar ta samu ne sakamakon inganta tsarin tattara bayanai, amfani da fasahar zamani wajen gudanar da ayyuka da kuma haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki.

Hukumar ta kuma ce ayyukan fitar da kaya zuwa ƙasashen waje a zangon farko zuwa na uku na shekarar 2026 sun samar da dala miliyan 752.85, wanda ya nuna ƙarin kashi 22.14 idan aka kwatanta da dala miliyan 586.15 da aka samu a makamancin lokacin 2025.

Bugu da ƙari, hukumar ta ce ta ƙwato haramtattun kayayyaki da waɗanda aka hana shigo da su da darajarsu ta harajin kwastam ta haura Naira biliyan 8.1, yayin da ta ƙaddamar da tsarin bayyana kuɗaɗen waje ta hanyar lantarki domin ƙara gaskiya da sa ido kan hada-hadar kuɗi.

Hukumar ta kuma bayyana cewa ta ceto namun dawa guda shida masu suna Pangolin a wasu samame a Jihar Ogun, inda ta miƙa su ga ƙungiyar Green Fingers Wildlife Conservation Initiative domin kula da su da kuma kare rayuwarsu.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *