Hukumar Wayar da Kan Al’umma ta Ƙasa (NOA) ta fitar da muhimman tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026, domin wayar da kan masu zaɓe, jam’iyyun siyasa da sauran masu ruwa da tsaki gabanin babban zaɓen Najeriya na 2027.

A cikin sanarwar da ta wallafa, hukumar ta ce dokar ta tanadi cewa dole ne a saki kuɗaɗen gudanar da zaɓe ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) aƙalla watanni shida kafin babban zaɓe, yayin da jam’iyyun siyasa za su miƙa jerin sunayen ’yan takararsu na ƙarshe kwanaki 120 kafin zaɓe.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa INEC za ta wallafa sahihan jerin sunayen dukkan ’yan takara kwanaki 60 kafin zaɓe, sannan masu zaɓe za su iya sauke katin zaɓensu (PVC) daga shafin hukumar.

Dangane da harkokin zaɓe, hukumar ta ce dokar ta tanadi gudanar da zaɓen fitar da gwani ta hanyar zaɓen kai tsaye ko cimma matsaya, tare da tilasta aika sakamakon zaɓe ta hanyar lantarki zuwa INEC.

Ta kuma bayyana cewa duk wanda aka samu da laifin sayen ƙuri’a zai fuskanci ɗaurin shekara biyu aƙalla ko tarar Naira miliyan biyar, yayin da cinikin katin zaɓe zai jawo tarar da ta tashi daga Naira miliyan biyu zuwa miliyan biyar.

Haka kuma, sanarwar ta bayyana ƙarin iyakokin kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe, inda ta ce an ɗaga kuɗin zaɓen shugaban ƙasa daga Naira biliyan biyar zuwa biliyan 10, na gwamna daga biliyan ɗaya zuwa biliyan uku, yayin da na kujerar sanata ya tashi daga Naira miliyan 100 zuwa miliyan 500.

Hukumar NOA ta ce tana tunatar da ’yan Najeriya masu shekarun kaɗa ƙuri’a da sauran masu ruwa da tsaki muhimmancin fahimtar tanade-tanaden dokar, domin sanin haƙƙoƙinsu da nauyin da ke kansu yayin gudanar da zaɓen 2027.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *