Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana damuwa kan ƙarancin albashin kansilolin ƙananan hukumomin babban birnin tarayya, tare da alƙawarin ɗaukar matakan magance matsalar.
Wike ya bayyana hakan ne yayin taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki a ƙaramar hukumar Kwali ranar Litinin, 9 ga Nuwamba, 2026.
- Wike ya yi alƙawarin ba kansilan da duk ya lashe mazaɓarsa Naira miliyan 10
- ’Yan sanda sun kubutar da mutum biyu da aka yi garkuwa da su a Yabo
Ya ce ya yi mamakin jin cewa albashin kansilolin Abuja bai kai na takwarorinsu da ke wasu jihohin Najeriya ba.
Ministan ya ce ba ya ganin ya dace a ci gaba da biyan kansilolin irin wannan albashi, musamman duba da nauyin aikin da suke gudanarwa.
A nasa ɓangaren, wakilin kansilolin 62 na Abuja ya roƙi ministan da ya sake duba albashinsu, yana mai cewa ba a yi wa kuɗin ƙarin girma ba tsawon kusan shekaru 19.